SHEIKH AMINA DAURAWA lectures  2.0 Icon

SHEIKH AMINA DAURAWA lectures

AdamsDUT Music & Audio
0
0 Ratings
17K+
Downloads
2.0
version
Nov 07, 2018
release date
62.4 MB
file size
Free
Download

What's New

new version with new features.

About SHEIKH AMINA DAURAWA lectures Android App

Wannan application yana dauke da wasu zababun lekcoci daga sheikh aminu ibrahim daurawa ke gabatarwa.shine muka ga ya dace muyi application wanda mutane zasu su saurara a saukake.
Allah ya sakawa Sheikh ibrahim aminu daurawa domin yayi kokari wajen yayi kokari wajen yada ilimin Allah da na manzon sa domin karuwar al'umar musulmai. Mukuma Allah ya bamu ikon ji da kuma amfani daga abin da muka saurara.
Bayan lectures na Sheikh ibrahim aminu daurawa akwai kudin tarihi kashi na daya da na biyu by Sheikh ibrahim aminu daurawa duk a cikin wannan manhaja idan akayi duba.
Akwai karatun malam Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 akan illar harshe,matsalolin aure by Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 dai sauransu.
za kuma a iya samun wasu karatuttukan na wasu malam irin su sheikh jafar mahmud adam, sheikh albani zariya,sheikh ali isah fantami, shiekh kabir gombe.

Wasu daga cikin karatuttukan sheikh jafar da za a samu idan akayi searching Adamsdut a play store.

Siffatus salatin nabiyyi sheikh jafar
Arbauna Hadith sheikh jafar mp3
Bulugul maram sheikh jafar mp3
Kitab Tauhid sheikh jafar mp3
Umdatul ahkam
Kitab at tauhid Hausa

Akwai karatun alqur'ani na wasu manyan makaranta kamar
complete quran offline by sheikh abdulrahman al-sudais
beautiful quran recitation by sheikh maher almuquiy
complete quran offline by shiekh abdolbasit
quran recitation by mishary alfasy mp3 offline and so on.
Don allah idan har kaji dadin wannan kundin tarihi by Sheikh ibrahim aminu daurawa to kayi sharing din sa ga sauran yan uwa musulmai domin suma su samu su amfana.
kuma kada a manta a yi rating kudin tarihi by Sheikh ibrahim aminu daurawa.

kadan daga cikin tarihin Sheikh ibrahim aminu daurawa,

TARIHIN SHEIK AMINU DAURAWA KANO :-Sunana Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal. Mahaifina
shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-
Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da
tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,
bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai. Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al-
Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32
unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala. Na fara karatun Alqur’ani mai girma tun ina dan
karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da
na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan
mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi
da fannoninsa daban-daban. Wadannan manyan malamai su ne:
1. Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
2. Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
3. Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
4. Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.
5. Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.
6. Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.
7. Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a
wajensa.
8. Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.
9. Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.
10. Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.
11. Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a
wajensa. Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa. Allah ya ji
qansa da rahama!
12. Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa. Wannan malami, a
wajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai
haquri da juriyar karantarwa.
da dai sauran malamai daban daban a duniya.

Other Information:

Requires Android:
Android 4.1+ (Jelly Bean, API 16)
Other Sources:

Download

This version of SHEIKH AMINA DAURAWA lectures Android App comes with one universal variant which will work on all the Android devices.

Variant
3
(Nov 07, 2018)
Architecture
Unlimited
Minimum OS
Android 4.1+ (Jelly Bean, API 16)
Screen DPI
nodpi (all screens)

All Versions

If you are looking to download other versions of SHEIKH AMINA DAURAWA lectures Android App, We have 2 versions in our database. Please select one of them below to download.

Loading..